13 Afirilu 2022 - 17:04
Ministan Harkokin Wajen Iraki Ya Iso Iran Domin Ziyarar Aiki

A yau Laraba ne ministan harkokin wajen na Iraki Fu’ad Hussai ya iso Tehran tare da tawagar da take rufa masa baya domin fara ziyarar aiki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iraki, Ahmad al-Sahhaf ya sanar da cewa; Daga cikin tawagar da take rufawa ministan baya da kawai shugaban hukumar tsaron kasar Kassim al-A’araji, da kuma wasu manyan jami’an tsaro.

Har ila yau kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iraki ya ce; Manufar ziyarar dai ita ce bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu.

342/